Wannan shine course din Blockchain Development na farko da Hausa a Duniya.
Inji DS Central, kuma zaka iya samun aiki a cikin wata 12 na farko idan kayi da gaske. Fasahar Blockchain, ‘Mahadi ka ture’ kamar yadda Marigayi Malam Nasir Mahuta ya kira ta, ta riga ta zama ruwan dare mai game duniya. Manyan kamfanonin takanoloji na duniya irinsu Meta, Google, da Microsoft, kawai zuba hannun jari suke a Blockchain development don su fada cikin Blockchain da karfinsu. Yanzu dukkan wadannan kamfanonin ai kowa da abinda yake ginawa, amma a ina suka yi kama? Inda suka yi kama gaba dayansu shine suna bukatar blockchain developers su taya su aiki su biya su. Blockchain developer jarumin mutum ne da ya kware wajen kera softuwayan blockchain. Dukkan software developer a duniya suna yin kaifin tunani da aiki na jarumta tukuru don hada software. Shi kuma blockchain developer yana nuna bajintar sa wajen samar da cryptocurrency, smart contracts, nfts, blockchains, scaling solutions, da sauransu.
- In dai ka kware, ana samun aiki da wuri saboda ana bukatar kwararrun developers
- Za ka zama mutum mai fasaha da kirkira, mutane zasu dinga sha’awar zama irinka saboda kwazonka da fasahar ka zata karu
- Ana samun kudade masu tsoka. Albashin su nada kauri. Manyan kwararru har dollar dubu dari uku ana biyansu a shekara. A hada smart contract guda daya kuma masu project zasu iya biyanka dollar dubu biyu ko sama da haka. Ana shiga hackathons kuma ana samun manyan kyaututtuka akan websites irin su Hackernoon, Dora Hacks, Devpost, da Techfiesta.
- Nan gaba ba lallai ka bukaci canja sana’a ba, tunda abubuwan cigaba suke, sai dai ka kara koyon sabbin dabaru
- Akwai mutane da yawa a fadin duniya da suke shirya su taimake ka iya komai, ka samu aiki. Kuma kai ma zaka taimaka wa communities. Watanni da yawa da na dauke kafa daga Facebook abinda na tafi ina koya shine Blockchain security Audit. Harkar cyber security ne amma a Blockchain. A wannan lokaci na fuskanci ba zaka iya hacking ba sai ka gane yadda developers suke hada smart contracts, shine yasa na je kuma na koyi solidity da smart contract development. Wannan ilimin ne nake so na juye muku shi a nan ciki awa dari don ku zama kwararrun developers wadanda ake alfahari dasu a duniya wajen gina blockchain infrastructure.
Manhajar simplilearn tace wadannan abubuwan ya kamata ace mutum ya iya in zai zama senior blockchain developer:
1. Design of the Blockchain Architecture: Blockchain Architecture, Ethereum Virtual Machine, Consensus Algorithms, Monolithic and Modular Blockchains.
Zan kara da: